Tsohon Firaministan Mali Soumeylou Boubeye Maiga ya Mutu
Tsohon firaministan Mali Soumeylou Boubèye Maïga – wanda ke fuskantar shari’a saboda tuhumar da ake masa ta cin hanci da rashawa – ya mutu yana mai shekara 67 da haihuwa.
Mista Maiga ya mutu ne ranar Litinin a wani asibiti a Bamako, babban birnin kasar, kamar yadda iyalansa suka sanar.
Iyalan nasa sun ce an kama shi kuma an tsare da shi karkashin wani hali mai tayar da hankali. A watan Disamba aka kwantar da shi a asibiti.
Read Also:
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ce gwamnatin ƙasar ta ki amincewa da bukatarsa ta zuwa kasashen waje domin a duba lafiyarsa.
Sai dai ta mika sakonta na ta’aziyya ga iyalan tsohon firaministan, bayan ta fitar da wata sanarwa da ke cewa ya mutu ne bayan wata doguwar jinya da ya yi.
An dai kama Mista Maiga ne a watan Agustan bara kuma aka tsare shi bayan da aka tuhume shi da aikata laifukan cin hanci da rashawa kan yadda aka sayo wani jirgin sama na shugaban kasa, yayin mulkin hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 53 minutes 23 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 34 minutes 48 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com