‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun yaba wa yunƙurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da janye tallafin man fetur.
Sun ɗauki matakin ne bayan gabatar da ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa Jimoh Olajide ya yi a zamanta na yau Talata.
Read Also:
Sakamakon haka ne Majalisar ta nemi ‘yan Najeriya da su yi haƙuri tare da yi wa gwamnati addu’a game da matakin.
A ranar Litinin ne – a jawabinsa na rantsuwar kama aiki – Shugaba Tinubu ya ce “tallafin man fetur ya ƙare”, yana mai cewa babu tanadin kuɗin a kasafin kuɗi na wata shidan ƙarshe na 2023.
Tuni jawabin nasa ya janyo dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar, inda mutane ke rige-rigen sayen man.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 46 minutes 34 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 27 minutes 59 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com