• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home General Yadda Sojojin Najeriya suka kashe ƴanbindiga sama da 1,000 a Agusta
  • General

Yadda Sojojin Najeriya suka kashe ƴanbindiga sama da 1,000 a Agusta

By
'ƴan Bindiga
-
August 29, 2024
Arewa Award

Rundunar Tsaron Najeriya ta ce sojojinta sun kashe ‘ƴan bindiga sama da 1,000 a cikin wannan watan a faɗin Najeriya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, inda a ciki ya bayyana cewa aikace-aikacen sojin yana matuƙar daƙile ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindigar.

“Muna sane cewa muna yaƙi ne da maƙiya marasa imani, wanda hakan ya sa dole mu ƙara ƙaimi wajen dakatar da su.”

Ya ce daga shirye-shiryen sojojin, akwai takura ƴan bindigar domin hana su sakat, “sannan sojojin suna bibiyar kwamandojin ƴan ta’addan da yaransu da ma masu taimaka musu.”

Ya ƙara da cewa tuni sun ga bayan wasu manyan kwamandojin ƙungiyoyin a watan “A Arewa ta Gabas an kashe irin Munir Arika da Sani Dilla (AKA Dan Hausawan Jibilarram) da Ameer Modu da Dan Fulani da Fari Fari da Bakoura Araina Chikin da Dungusu da Abu Darda da Abu Rijab.”

Read Also:

  • Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah
  • Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a yankin Arewa maso Yamma sojojin sun ga bayan manyan ƴan bindiga kamar su Kachalla Ɗan Ali Garin Fadama da Kachalla Ɗan Mani Na Inna da Kachalla Basiru Zakariyya da Sani Baka Tsine da Inusa Zangon Kuzi da Ibrahim da Tukur da Kamilu Buzaru da sauransu.

“Sojoji sun samu gagarumar nasara a kan ƴan bindigar, sannan kuma suna ci gaba da ƙara ƙaimi a aikace-aikacen da suke yi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas domin magance matsalar tsaron da ake fama da su.”

Ya ce jimilla a watan Agusta, sojoji sun kashe ƴan ta’adda 1166, an kama guda 1,096 sannan an tseratar da waɗanda aka kama guda 721.

Haka kuma a cewar sanarwar, ak ƙwato makamai 391, da alburusai 15,234, sannan sun daƙile satar mai da aka ƙiyasta ya kai na Naira biliyan 5.

“Aikace-aikacen sojojin sun sa ƴan bindigar sun ja baya sosai, wanda hakan ya sa suke ta miƙa wuya, musamman a Arewa maso Gabas,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa sojojin za su ƙara matsa lamba a sauran yankunan domin samun irin wannan nasarar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • Agusta
  • Edward Buba
Previous articleSojoji sun hallaka ‘Yan Ta’adda 8 a jihar Kaduna
Next articleGwamnatin Najeriya ta bai wa ƴan kasuwa wa’adin rage farashin kayayyaki
'ƴan Bindiga

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah

Gwamnonin PDP na taro a Zamfara

Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

kotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele Kyari

Ana neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a Sokoto

A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati – ASUU

EFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsare

Atiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi

PDP ta zargi APC da yunkurin kawo tasgaro a Damukradiyya

Hoton Tinubu

Fadar Shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu

Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje da dama a Filato

Gwamnati ta yi hasashen samun ambaliya a jihohin Najeriya 19

Recent Posts

  • Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah
  • Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai
  • Gwamnonin PDP na taro a Zamfara
  • Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1529 days 11 hours 43 minutes 37 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1511 days 13 hours 25 minutes 2 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Bama goyan bayan ayyukan ta'addanci a Najeriya - Miyetti AllahSojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a KatsinaShalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kaiGwamnonin PDP na taro a ZamfaraYa kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai - MusaHukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kanokotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele KyariAna neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a SokotoA biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUUAmurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyiEFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsareMajalisar Dokokin Kano ta Dakatar da Ciyaman din RanoƘananan dillalan mai sun zargi shugabanninsu da yiwa Matatar Dangote zagon ƙasaAtiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi
X whatsapp