Home AFIRKA Shugaban Comoros ya tsallake ‘rijiya da baya’

Shugaban Comoros ya tsallake ‘rijiya da baya’

Shugaban Comoros, Azali Assoumani  ya ɗan ji rauni bayan da wani ya kai masa farmaki da wuƙa a jiya Juma’a, kamar yadda kakakin gwamnatin ƙasar ta bayyana, tana mai cewa an kama maharin.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 agogon GMT a Salimani Itsandra wani gari da ke arewacin babban birnin ƙasar, Moroni, inda shugaban ya je ta’aziyar rasuwar wani babban malamin addinin Islama na ƙasar, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana wa kamfanin dilancin labarai na Reuters.

Kakakin gwamnatin, Fatima Ahamada ta ce shugaba Assoumani ba ya cikin haɗari sakamakon raunin, kuma tuni ya koma gida.

Ganau sun ce maharin wani matashi ne mai shekaru 22, wanda ba shi da tarihin aikata laifi, kuma ya shiga aikin soja a shekarar 2022.

Wuƙar ta ji wa shugaban rauni, amma wani daga cikin mutanen da ke  zaman makoki ya kama maharin.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp