Gwamnatin mulkin sojin Mali ta ce ta yi nasarar daƙile wani harin ta’addanci a babban birnin ƙasar, tana mai cewa yanzu hankula sun kwanta.
Rundunar sojin ƙasar tana gudanar da aikin tabbatar da tsaro bayan fafatawar da ta yi da ƴan bindigar da suka ƙaddamar da farmaki kan wata Cibiyar Ƴan sanda a Bamako.
A sanyin safiyar wannan Talatar ce, ƴan bindigar suka kai farmakin a kusa da filin jiragen sama kamar yadda wasu da suka shaida lamarin suka bayyana, inda suka tabbatar cewa, lallai sun ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashen bama-bamai.
Read Also:
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya rawaito cewa, an kulle filin jiragen saman na wani ɗan lokaci sakamakon fargabar abin da ka iya faruwa.
Tuni rundunar sojin ƙasar ta buƙaci mazauna yankin da su yi ƙaura na wucen-gadi kafin fitar da wata sabuwar sanarwa nan gaba.
Tun bayan juyin mulkin 2021, gwamnatin mulkin sojin Mali ke yaƙi da ƙungiyoyin ƴan ta’adda da suka haɗa da ƴan aware da mayaƙan jihadi masu alaka da al-Qaeda da ISIL.
A ƙarƙashin jagorancin shugaban mulkin sojin Mali, Kanar Assimi Goita, ƙasar ta yanke hulɗa da aminanta na ƙasashen Turai da kuma tsohuwar uwargijiyarta, Faransa, inda ta karkata hankalinta kan kulla alaƙa da Rasha da sojojin haya na Wagner domin samun agaji a fannin yaƙi da ƴan ta’adda.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 1 minute 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 42 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com