Uganda na yin asarar kuɗin da ya kai Dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 500 a duk shekara saboda cin hancin, kwatankwacin kaso 1 bisa 4 na kasafin kuɗin da ƙasar ke yi, kamar yadda hukumar da ke yaƙar cin hanci a ƙasar ta tabbatar.
A cewar shugabar hukumar yaƙi da cin hanci ta Uganda Beti Kamya Turwomwe, ƙasar na asarar sama da tiriliyan 9 da miliyan 100 na kuɗin ƙasar Shiling, kwatankwacin dala biliyan 2 da miliyan 500 a duk shekara.
Ta ce wannan ya kai kaso 23 cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar, abin da ke zama wani babban ƙalubale ga ayyukan daƙile cin hanci a ƙasar.
Cin hanci da rashawa wata gagarumar matsala ce da ke addabar gabashin Afirka.
Read Also:
Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Musaveni ya sha nanata alwashin ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar cin hanci ganin yadda matsalar ta ratsa cikin jami’an gwamnati.
Turwomwe ta ce sashin da ta ke jagoranta ya samu nasrar ƙwato dala miliyan 2 da aka wawushe, inda ta nuna damuwa kan rashin sanya kuɗi a hukumar da take jagoranta.
Wannan kalaman nata ya biyo bayan rahoton shekara-shekara da ake fitarwa na cibiyar bincike kan tabbbatar da ganin an yi ayyukan gwamnati a buɗe babu kumbiya-kumbiya.
Rahoton na zuwa mako guda da shugaban Uganda Yoweri Musaveni ya sanar da yafewa wasu manyan jami’an gwamnati da aka ɗaue shekara 10 saboda kamasu da badaƙalar dala miliyan 1 da miliyan 200.
Musaveni ya yafe musu bayan sun kammala shekara 5 a gidan 5, abinda ya tunzura kungiyoyin fararan hula
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 56 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 38 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com