Fararen hula 10 sun mutu sakamakon harin ƴan ta’adda a Burkina Faso

Wasu da ake zargi yan ta’adda masu ikirarin jihadi ne sun kashe fararen hula 10 a wata kasuwa da ke arewacin ƙasar ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda jami’an yankin su ka bayyana a ranar Talata.

Wasu mazauna lardin Gnagna inda lamarin ya faru ssun ce ƴan ta’addan sun farmaki garin ne da yammacin Lahadi, inda su ka kashe mutane tare da raunata da dama.

Wani jami’in asibiti a yankin ya ce yana da matuƙar wahala a tantance adadin waɗanda su ka mutu, amma ya ce  akalla mutane 10 sun mutu, kana 50 su ka jikkata.

Ganau sun ce maharan sun sun shiga garin ne kuma su ka fara harbi kan uwa da wabi, inda su ka tarwatsa jama’a, har su ka fara fasa shaguna su na sata.

Ƙasar da ke yankin yammacin nahiyar Afrika tana fama da matsalar ƴan ta’adda masu ikirarin jihadi da su ka kwarara daga makwafciyarta Mali tun daga shekarar 2015.

Dubban fararen hula, sojoji da yan sanda ne aka kashe, lamarin da ya fusata wasu hafsoshin soji har su ka yi juyin mulki  a shekarar 2022.

Sama da mutane dubu 26 ne su ka mutu sakamakon hare-haren ƴan ta’adda a Burkina Faso tun daga shekarar 2015, fiye da dubu 6 daga cikin su a wannan shekarar aka kashe su.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 44 minutes 31 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 25 minutes 56 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com