Shugabannin ƙasashen Benin da Senegal sun gana don farfaɗo da alaƙarsu

Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya kai wata ziyarar aiki na yini guda ƙasar Benin da yammacin jiya Talata, da nufin ƙarfafa dangantaka da farfaɗo da haɗin gwiwa tsakanin Benin da Senegal.

Shugaba Patrice Talon ya nuna farin cikinsa da wannan ziyarar, musamman da tazo kwanaki kaɗan gabanin bikin tunawa da ranar ƴancin ƙan ƙasar.

Anasa ɓangaren Bassirou Diomaye Faye ya bayyana goyon bayan ƙasarsa ga yaƙin da Benin ke yi da ƴan ta’adda, tare da fatan ƙasashen biyu za su samu ci gaba mai ɗorewa a fannin kasuwanci.

Dangane da Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS kuwa, Faye ya tunanar da shugaba Talon irin ƙalubalen da ƙungiyar ke fuskanta, acewarsa dole ne kamar UEMOA, sai an kawo sauye – sauye domin tunkarar halin da ake ciki yanzu haka.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da wani shugaban ƙasar Senegal ya kai Cotonou tun bayan da Patrice Talon ya hau kan karagar mulki a shekarar 2016.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com