Gwamnan jihar Filato kuma Babban Daraktan yakin neman zaben dan takarar shugabancin Nijeriya karkashin inuwar jam’iyyar APC, Simon Bako Lalong, ya bayyana cewa fafaroma bai fada masa zunubi bane karbar mukamin daraktan yakin neman zaben jam’iyyar APC ba.
Lalong yace har yanzu shi cikakkeb kirista ne kuma mabiyin Darikar Katolika duk da hukuncin da ya yanke na jagorantar yakin neman zaben takarar shugaban kasa da mataimakin a APC na Musulmi da musulmi.
Read Also:
Ya kuma bayyana hakan ne jin kadan bayan ganawa da shuugaban kasa Muhammadu Buhari, domin nuna godiyar sa bisa amince da jami’ar Jos a matsayin cibiyar kula da cutar daji ta kasa, inda yayi ikirarin cewa a matsayin sana mai kishin addinin katolika, wanda kuma yayi Baftizma yana da babbar lambar yabo mai girma daga fadar Fafaroma Knight, ta Saint Gregory, fafaroma bai fada masa cewa ba daidai bane ya zama shugaban yakin neman Zaben musulmi da musulmi ba.
“Matsayin mu na mabiya darikar katolika, duk abinda za muyi muna neman shawarar Fafaroma. Kuma Fafaroman bai fadamin abinda nayi na karbar wannan mukamin laifi bane, muna karbar umarnin, kamar yadda yace”.
Lalong ya kara da cewa bai taba neman kasancewa dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Bola Tinubu ba a shekarar 2023.
“Maganar gaskiya ni dan Jam’iyyar APC ne, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Jam’iyyar, kuma bana zagon kasa ga Jam’iyya ta, bana barar a bani mataimakin shugaban kasa, kwarai wasu mutane sun rubuta takardar bukatar mataimakin a madadi na, amma abinda na kawai na bukata shine tkitin sanata.
“Na sami tikitin takarar sanata da nake jira. Don haka idan a wasu mutane nada Muradin zama mataimakin shugaban kasa, kuma basu samu ba, amma suna so suyi amfani da addini domin cika burin su, baza suyi amfani dani ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 50 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 31 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com