Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC, ta bude kofa ga masu sha’awar sayan wasu kaddarorin gidade da filaye 160 a jahohin kasar 12 da aka kwace daga wajen wadanda aka zarga da cin hanci da rashawa.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, babban birnin kasar.
Tuni dai wasu suka fara kiran gudanar da bincike wajen gano sahihancin kudaden wadanda za’a sake saida wa irin wadan nan kaddarori.
A bayan bayan nan ne rahotanni daga Najeriya ke cewa EFCC za ta yi gwanjon gidaje da filaye 144 da aka kwace a fadin kasar, inda jihohin Legas, Abuja da kuma Jihar Ribas ke kan gaba.
Kakakin EFCC ya bayyana cewa daga cikin kadadrorin, akwai gidaje 24 da ke rukunin gidaje na Banana Island, sai 21 a Thornburn, Yaba, duka a Legas,sai kuma 6 na a Court Estate da ke birnin Fatakwal.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 3 hours 19 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 5 hours 1 minute 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com