Babban Sakataren hukumar dake lura da Jami’oi a Nijeriya NUC Farfesa Abubakar Adamu Rasheed a ranar Litinin ya kaddamar da tagwayen dakunan daukar darasi wanda aka sanya sunan sa a jami’ar Maryam Abacha American University ta Nigeria (MAAUN), Kano.
Farfesa Rasheed a yayin da yake kaddamar da ginin, ya bayyana gasuwarsa da irin kayayyakin da aka zuba a cikin ta, ya kuma godewa hukumar gudanarwar Jami’ar bisa sanya mata sunan sa da tayi.
Ya kuma yaba da gudunmawar farfesa Adamu Abubakar Gwarzo na daga darajar fannin ilimi a Nijeriya da sauran kasashe.
Farfesa Rasheed ya sami damar zagayawa wasu gine-gine a cikin Jami’ar da suka hadar da dakin karatu na Murtala Ramat, filin wasa na Mohammed Ibrahim Usman Yakasai da dai sauransu.
Yayin ziyarar Farfesa Rasheed ya sami tarbar farfesa Prof. Gwarzo, Matainakin shugaba Jami’ar a fanni Gudanarwa Dr. Habib Awais Abubakar, sai mataimaki na fannin harkokin Jami’ar da walwalar dalibai Dr. Hamza Garba and Prof. Ibrahim Usman Yakasai.
Da dai sauran shuwagabanni sashe daban-daban na Jami’ar ta MAUUN dake jihar Kano.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 4 hours 26 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 6 hours 8 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com