Rahotannin daga Nijeriya na bayyana cewa Kotun koli ta tabbatar da Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya matsayin ‘dan takarar sanata na yankin Yobe ta arewa a karkashin jam’iyyar APc a zabe mai zuwa,
A hukunci mafi rinjaye da aka yanke a ranar Litinin, kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka kara wacce ta ayyana Bashir Machina matsayin ‘dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa a APC.
Jam’iyyar APC na ƙalubalantar Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa.
Jam’iyyar ta kafe cewa shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne halastaccen ɗan takararta a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
Read Also:
A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam’iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.
Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.
Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen.
Ya kuma ce kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.
To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce yana fatan Kotun Ƙolin za ta yi watsi da ƙarar sakamakon rashin ƙwararan hujjoji, kasancewar Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 14 hours 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 15 hours 42 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com