Shugaban Najeriya zai iya dakatar da gwamna – Kotun Ƙoli

Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci cewa shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓen jami’in gwamnati a lokacin da aka ayyana dokar ta ɓaci a wata jiha.

Hukuncin ya fito ne a ranar Litinin daga kwamitin alƙalai bakwai, inda alƙalai shida suka amince da matsayar kotun, yayin da alƙali guda ɗaya ya bayar da ra’ayi na daban.

Karar dai ta fito ne daga gwamnatin jihar Adamawa tare da wasu jihohi guda goma da gwamnoninsu ke ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Sun ƙalubalanci matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers a watan Maris na wannan shekara, tare da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da dukkan ‘yan majalisar jihar na tsawon watanni shida.

Masu ƙarar sun yi hujjar cewa ƙundin tsarin mulki bai ba wa shugaban ƙasa ikon dakatar da jami’an da aka zaɓa da ke kan mulki ba. Sai dai, a hukuncin da Alƙali Mohammed Idris ya karanta, Kotun ta bayyana cewa Sashe na 305 na ƙundin tsarin mulki ya bai wa Shugaba damar ɗaukar “matakan gaggawa” domin dawo da zaman lafiya da daidaito a duk inda aka ayyana dokar ta ɓaci.

Kotun ta ce tunda ƙundin tsarin mulkin bai fayyace irin matakan gaggawar da za a ɗauka ba, hakan na bai wa shugaba damar amfani da fahimtarsa wajen yanke hukunci kan matakin da ya dace.

Duk da haka, alƙali ɗaya daga cikin kwamitin ya yi fatali da wannan matsaya, inda ya ce ko da yake Shugaba na da ikon ayyana dokar ta ɓaci, bai kamata ya yi amfani da ikon wajen dakatar da jami’an da aka zaɓa kuma ke kan mulki kamar gwamna da ‘yan majalisa ba.

Wannan hukunci ya zo kusan watanni uku bayan an kawo ƙarshen dokar ta ɓaci a jihar Rivers tare da mayar da gwamnan da majalisar jihar kan mukamansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com