DalilinTanzania na dakatar da jaridar The Citizen a kasar

Gwamnatin Tanzania ta dakatar da wata jarida da ke kan gaba a ƙasar da ake wallafawa a shafin internet, bayan ta wallafa hotunan da ke alakanta shugabar ƙasar, Samia Suluhu Hassan da sace-sace da kuma kashe kashen ƴan adawa da aka yi a baya-bayan nan.

Ɗaya daga cikin hotunan bidiyo da jaridar The Citizen ta wallafa  ya nuna shugaba Samia Suluhu Hassan zaune tana kallon bidiyon cin zarafin da aka yi wa ƴan adawa haɗe da wasu da ba su ji ba basu gani ba.

Gabanin faruwar lamarin shugabar ƙasar ta fuskanci caccaka daga ciki da wajen Tanzania game da zarge-zargen da ake yi wa jami’an tsaron ƙasar da alhakin yin garkuwa tare da kashe wasu daga cikin jiga jigan jamiyyar adawa na ƙasar.

Tuni dai jaridar ta cire tallace-tallacen da ta wallafa, kana ta fitar da sanarwar da ke cewa manufarsu ita ce bayyana damuwar allummar ƙasar a game da matsalolin tsaro.

A ranar Laraba ne The Citizen da ke kan gaba daga cikin jaridun da ake walafawa da harshen Turanci a Tanzania ta fitar da sanarwar dakatar da ayyukanta na tsawon kwanaki 30 da hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta  Tanzaniya ta yi.

Tun a cikin watan Agustan da ya gabata ne dai, gwamnatin Samia Suluhu Hassan ta haramta manyan gangami biyu da jam’iyyar Chadema ta ƙaddamar, sannan ta sanar da batun tsare shugabannin jam’iyyar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 13 hours 54 minutes 8 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 35 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com