Gwamnatin Senegal ta ƙaddamar da shirinta mai nisan zango na ciyar da ƙasar gaba, wanda take fatan za a kammala aiwatar da shi cikin shekaru 25 masu zuwa.
Sai dai gwamnatin Senegal ɗin ta bayyana wasu daga cikin muradun da tsara cim-musu cikin shekaru 5.
Muhimman muradun da take fatan cim-musu a gejeren zango kuwa, sun haɗa da rage nauyin bashin da ke kan ƙasar daga kaso 83.7 zuwa kaso 70 cikin 100.
Read Also:
Sai kuma rage giɓin kasafin kuɗi zuwa kashi 3 nan gaba kaɗan, saɓanin giɓin kashi 10.4 da ƙididdiga ta nuna cewar gwa,natin senegal din ta yi fama da shi daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Ƙalubale na gaba da gwamnatin Senegal ta sha alwashin magancewa shi ne matsin rayuwa, inda ta yi alƙawarin cikin shekaru biyar da ke tafe, za ta ƙara yawan matsakaicin albashin da ‘yan ƙasar ke samu da kashi 50 cikin 100, kwatankwacin ƙarin daga dala dubu 1, 660 zuwa aƙalla dala dubu 2,648, yayin da kuma za a rage hauhawar farashin kayayyaki zuwa kashi 2 cikin shekaru 5.
Shugaban Senegal Basirou Diomaye Faye da Fira Ministansa Ousmane Sonko ne suka jagoranci kaddamar da gagarumin shirin a garin Diamniadio, mai nisan kilomita 30 daga Dakar babban birnin ƙasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 37 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 12 hours 18 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com