Home AFIRKA Kotu tayi watsi da bukatar mataimakin shugaban Kenya kan yunkurin tsige shi

Kotu tayi watsi da bukatar mataimakin shugaban Kenya kan yunkurin tsige shi

Kotu a Kenya ta yi watsi da buƙatar da mataimakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua ya gabatar, inda yake nema a hana Majalisar Dattawan gudanar da mahawara da kuma kaɗa  kuri’a domin tsige shi.

Lokacin da yake yanke wannan hukunci a jiya talata, alƙalin babbar kotun mai shari’a Enock Chacha Mwita, ya ce ta la’akari da abubuwan da ke ƙunsh a kundin tsarin mulki, majalisar dokoki tana da damar gudanar da bincike kan duk wani zargi da ake yi wa mataimakin shugaban ƙasa, saboda haka yunƙuri domin hana wannan bincike zai kasance iya kasancewa karen-tsaye ga dokokin ƙasar.

To sai dai duk da cewa bai kasance a cikin zauren shari’ar ba, amma lauyen da ke kare mataimakin shugaban ƙasar ya ce za su ɗaukaka don nuna rashin gamsuwa a game da wannan hukunci.

Tun a cikin makon jiya ne ƙaramar majalisar dokokin Kenya ta kaɗa ƙuri’ar tsige Mista Gachagua mai shekaru 59 a duniya, saboda a cewarta ta same shi da laifin ƙin yi wa shugaban ƙasa William Ruto biyayya sannan kuma ya handame dukiyar al’umma.

Kamar dai yadda yake rubuce a cikin kundin tsarin mulki, ana buƙatar ƙuri’u 45 daga cikin 68 da ake da su a cikin majalisar dattawa ne domin tsige mataimakin shugaban, kuma idan hakan ya tabbata, Rigathi Gachagua zai kasance mataimakin shugaban ƙasar Kenya na farko da aka tuɓe daga mukaminsa a tarihin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp