Jami’an gwamnatin Sudan ta Kudu na gudanar da ganawar gaggawa sa’o’i bayan sanar da ɗage zaɓen ƙasar zuwa nan da shekara biyu masu zuwa.
A baya an tsara gudanar da zaɓukan cikin watan Disamba mai zuwa.
A shekarar 2018 aka cimma yaryajejeniyar zaman lafiya da ta bai wa shugaban ƙasar, Silva Kiir damar ci gaba da zama shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, yayin da tsohon abokan hamayyarsa, Riek Machar ya zama mataimakinsa.
Ƙasar Sudan ta Kudu ba ta taɓa gudanar da babban zaɓe ba tun bayan ɓallewar ƙasar a 2011.
Matakin jinkirta zaɓen zuwa shekara biyu nan gaba, bai zowa da jama’a da ‘yan ƙasar da mamaki ba.
Shugabannin siyasar ƙasar ba su shirya wa gudanar da zaɓukan a ƙasar ba.
Hakan ne ma ke ƙara haifar da shakkun cewa suna ƙoƙarin tabbatar da kansu a ikon ƙasar mai arzikin man fetur.
Ofishin shugaban ƙasar ya ce ya kamata a gudanar da wasu muhimman abubuwa kamar rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar kafin gudanar da zaɓen.
Haka kuma jami’an ƙasar sun bayyana matsalolin tsaro da rashin shiryawa zaɓen a matsayin hujjar ɗage zaɓen.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 13 hours 46 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 28 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com