Mahukuntan Chadi sun ja hankalin al’umma sakamakon cikar wasu koguna

Mahukuntan Chadi sun yi kira ga al’ummar ƙasar su kasance a faɗake bayan da wasu koguna suka cika maƙil har su ke barazanar tumbatsa, a yayin da kasar ke ƙoƙarin murmurewa daga ambaliyar da ta kashe mutane sama da ɗari 5 kwanakin baya.

Fira minista, Allamaye Alina ya ce ruwan kogin Chari ya ƙaru da sama da mita 8, kwatankwacin ƙafa 26 a cikin kwanaki 10 da suka gabata.

Babban birnin Chadi, N’Djamena,  yana kusa ne da inda kogunan Logon da Chari suka yi magama, kuma dukannin kogunan sun cika sakamakoln mamakon ruwan sama da ake ta yi.

Tun a watan Yuli ƙasar ta fuskanci mummunar ambaliya, wadda ta lalata gidaje dubu dari da 64 da kadada dubu ɗari 2 da 50 na filayen noma.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com