Madugun adawa na jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, Anicet-George Dologuele yayi watsi da sakamakon zaɓen ƙasar da ke bayyana shugaba Faustin-Archange Touadera a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen watan jiya.
Tun gabanin sakamako Touadera mai shekaru 68 shi ne aka yiwa tsammanin ya lashe zaɓen yayinda sakamako ya nuna shi a matsayin wanda ya samu fiye da kashi 76 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Nasarar kai tsaye ta baiwa Touadera damar ci gaba da mulki a wa’adi na 3, bayan da tun a watan Oktoban bara ya sanar da aniyar sake tsayawa takara lamarin da ƴan adawa ke yiwa kallo a matsayin wani yunƙurin ci gaba da mulkin kama karya a ƙasar.
Read Also:
Sai dai madugun adawar Dologuele wanda ya samu kashi 15 na yawan ƙuri’un da aka ƙada a zaɓen da ya bashi damar zuwa na biyu ya ce an tafka maguɗi ne a zaɓen tare da sauya sakamako.
A cewar Dologuele ba a baiwa jama’a sakamakon abin da suka zaɓa ba, ta yadda hukumar zaɓe ta yi zuraren ƙuri’u a wasu wuraren don nuna shugaban a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Shugaba Faustin-Archange Touadera wanda ke samun cikakken goyon bayan Rasha da ta tallafa masa wajen kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar ke fuskanta kai tsaye nasarar ta bashi damar ci gaba da jan ragamar ƙasa har zuwa ƙarin shekaru 5 a wa’adi na 3.
Ana kallon nasarar da ya yi ta kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a jamhuriyyar Afrikan ta tsakiya ya taimaka masa matuƙa wajen samun cikakken goyon bayan jama’a.










